in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi ya yi kira da a bunkasa tsarin diflomasiyya mai halayya ta musamman ta kasar Sin
2017-12-29 09:32:30 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira ga jakadun kasarsa dake aiki a ofishoshin jakadancin kasashen waje daban daban, da su kara azama, wajen aiwatar da manufofin diflomasiyyar kasar ta Sin mai halayya ta musamman.

Shugaba Xi wanda ya gana da jakadun a jiya Alhamis, ya ce a madadin kwamitin koli na JKS, yana gabatar da gaisuwa da jinjina ta musamman ga jakadun na Sin bisa kwazonsu, da irin dimbin nasarori da suka cimma cikin shekaru 5 da suka gabata.

Ya ce yayin da kasar Sin ke shiga sabon zamani karkashin mulkin guguzu mai salo na musamman, yana fatan jakadun kasar za su zage damtse wajen aiwatar da manufofin taron wakilan JKS karo na 19 da ya gabata, su kuma fahimci yanayin da ake ciki a mataki na kasa da kasa game da sha'anin diflomasiyya.

Har ila yau shugaban na Sin ya ce ya zama wajibi jami'an diflomasiyya su zamo masu biyayya ga jam'iyya da kuma kasarsu. Daga nan sai ya bukace su da su dora muhimmanci ga ci gaban jakadanci mai samar da moriya ga dukkanin sassa, da bunkasa hadin gwiwa, tare da ba da gudummawar gina al'ummar duniya mai makoma guda. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China