in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Sin da Aljeriya sun nuna farin ciki game da nasarar harba tauraron dan adam na Alcomsat-1
2017-12-11 09:17:23 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na Aljeriya Abdelaziz Bouteflika, sun taya juna murna game da nasarar da aka cimma, ta harba tauraron dan Adam na sadarwa mai lakabin Alcomsat-1 na kasar Aljeriya.

An dai harba tauraron ne daga cibiyar harba tauraron dan Adam dake Xichang a lardin Sichuan dake kudu maso yammacin kasar Sin, da sanyin safiyar Litinin.

A sakon sa game da hakan, shugaba Xi ya bayyana shirin harba tauraron na Alcomsat-1, wanda shi ne tauraron dan Adam na sadarwa irin sa na farko da kasar Aljeriya ta mallaka, a matsayin muhimmiyar alama dake nuna ingantacciyar alakar dake tsakanin Sin da Aljeriya.

Shugaba Xi ya ce, alakar sassan biyu wadda a wannan lokaci ta shafi harkar kimiyyar sararin samaniya, za ta taka rawar gani wajen bunkasa tattalin arzikin kasar Aljeriya, ta kuma inganta rayuwar al'ummar kasar tare da kara kyautata zamantakewar su.

Ya ce, shekarar 2018 dake tafe, za ta kasance ta cika shekaru 60 da kafuwar huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Aljeriya, kuma Sin na fatan ci gaba da karfafa musaya tsakanin ta da Aljeriya a dukkanin fannonin ci gaba, ta yadda al'ummun kasashen biyu za su ci gajiyar hakan.

A nasa bangaren, shugaba Bouteflika ya ce, nasarar harba Alcomsat-1, ta tabbatar da kyakkyawar nasarar hadin gwiwar kasar sa da Sin, alakar da ya bayyana a matsayin ta gargajiya mai kuma dadadden tarihi.

Shugaba Bouteflika ya ce, kasar sa, za ta ci gaba da hulda da Sin musamman a fannin inganta hadin gwiwa a dukkan sassa, domin cimma moriyar juna.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China