Jami'in wanda ya bayyana hakan jiya Laraba a birnin Maiduguri, fadar mulkin jihar Borno, ya ce an kasa shirin riga kafin ne gida biyu
Kwamishinan ya kara da cewa, a cikin makonni ukun da suka gabata gwamnati ta samar da sama da maganin cutar kwalara 950,000 wadanda aka digawa mutane da nufin dakile yaduwar a jihar.
Gwamnan jihar Borno tare da hadin gwiwar hukumar lafiya ta duniya da sauran abokan huldarta a fannin samar da agaji, sun yi nasarar dakile yaduwar cutar. (Ibrahim)