in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta sake bude kofa don habaka harkokin zuba jari daga kasashen waje
2017-07-29 12:56:12 cri

Kasar Sin na kokarin kara jawo hankalin masu zuba jari kai tsaye na kasashen waje da masana masu bada hidima na kasashen waje ta hanyar fadada damar kasuwanci da inganta yanayi.

An cimma wannan matsaya ce yayin taron majalisar zartarwar kasar da ya gudana jiya Jumma'a karkashin Firaminista Li Keqiang.

Za a fara aiwatar da shirin fitar da jerin kamfanonin da kayayyaki da sauran abubuwa wadanda ba su da damar isa kasuwannin a duk fadin kasar Sin, wanda tuni a fara amfani da shi a yankunan kasuwanci 11 marasa shinge a kasar, sannan za a bude karin bangarori da za a iya zubawa jari.

Baya ga haka, akwai tabbacin ribar da ake samu za ta samu damar fita daga kasar ba tare da matsala ba.

Domin kara jan hankalin masana na kasashen waje, zuwa rabin karshe na shekarar nan, Gwamnati za ta samar da wani tsarin izinin aiki ga baki dake aiki a kasar, tare da cikakken bayani kan yadda za a nemi visa, a wani yunkuri na inganta amfana daga kwarewarsu.

Za kuma a bada visar shekaru 5 zuwa 10 mai izini shiga da fita da dama ga baki masu aiki a kasar Sin, wadanda za su nemi izini aiki ko shaidar zama.

Li Keqiang ya ce shigowar kudaden jari daga ketare, ya taimaka wajen samar da ci gaban kasar cikin sauri.

Ya ce kamfanonin kasar su ne ke kasa a duniya, don haka, dole ne a aike da sako mai karfi na jan hankalin masu zuba jari. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China