A cewar hukumar kwastom ta Urumqi, a watan Yuli kadai, an fitar da kayayyaki kimanin dubu 176 daga yankin na Xinjiang tun daga lokacin da yankin ya fara aiwatar da shirin cinikayya da kasashen ketare ta hanyar zamani.
Guo Ying, jami'in hukumar kwastom na Urumqi ya bayyana cewa, ko da yake, yankin ya fara gudanar da harkokin kasuwancin da kasashen ketare ta hanyar zamani a makare, amma akwai gagarumin ci gaba da za'a samu a nan gaba.
Kayayyakin da suka hada da kayan kyale-kyale na mata, da na'urorin lantarki da batura na daga cikin irin kayayyakin da aka fitar da su daga yankin zuwa kasar Rasha da tsakiyar Asiya. (Ahmad Fagam)