in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana kidaya kuri'u bayan kammala zagaye na biyu na zaben shugaban kasar Liberia
2017-12-27 10:38:04 cri
Bayan kammala zagaye na biyu na zaben shugabancin kasar Liberiya, yanzu haka ana ci gaba da kidaya kuri'un da aka kada a dukkan rumfunan zaben kasar.

Tun da misalin karfe 6 na yammacin ranar Talata ne aka fara kidaya kuri'un, bayan da aka rufe rumfunan zaben kasar kimanin 5,390 dake fadin kasar ta yammacin Afrika.

Masu sanya ido a zaben na cikin gida da na kasashen waje sun bayyana zaben da cewa an gudanar da shi cikin kwanciyar hankali da lumana. Idan aka kwatanta da babban zaben shugaban kasar wanda ya gudana a ranar 10 ga watan Oktoba, inda aka samu matukar fitowar masu kada kuri'a, sai dai a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar ba'a samu yawan jama'a ba.

A babban birnin kasar Monrovia, an girke jami'an tsaro masu yawan gaske a dukkanin rumfunan zaben.

An fafata a zagaye na biyu na zaben ne tsakanin dan takarar jam'iyyar adawa ta (CDC) George Weah, da mataimakin shugaban kasar Liberiyan Joseph Boakai, kana dan takara na jam'iyya mai mulkin kasar.

Duk wanda ya yi nasarar lashe zaben shi ne zai maye gurbin Ellen Johnson Sirleaf, wadda ta kasance shugabar kasa mace ta farko a nahiyar Afrika, za ta sauka daga mulki ne bayan kammala wa'adi na biyu a shugabancin kasar. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China