in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An shirya gudanar da zagaye na 2 na zaben shugaban kasar Liberia a ranar 26 ga watan Decemba
2017-12-13 13:35:12 cri
Shugaban hukumar zaben Liberia Jerome Korkoya, ya ce an shirya gudanar da zagaye na 2 na zaben shugaban kasar a ranar 26 ga wannan watan.

Jerome Korkoya ya shaidawa manema labarai jiya a Monrovia cewa, hukumarsa za ta tabbatar da gudanar da sahihin zabe mai cike da adalci.

A baya, an tsara gudanar da zaben ne a ranar 7 ga watan Nuwamba, amma sai kotun kolin kasar ta bada umarnin dakatarwa, bisa korafin da wasu jam'iyyu suka shigar gabanta bayan kammala zageye na farko a ranar 10 ga watan Oktoba.

A cikin korafin, jam'iyya mai mulki ta Unity da jam'iyyar adawa ta Liberty, sun yi kira da a sake gudanar da zaben. Sai dai, kotun kolin ta yi watsi da bukatar, inda a makon da ya gabata ta dage umarnin dakatarwa da ta bayar.

Zagaye na 2 na zaben, zai gudana ne tsakanin dan takarar jam'iyyar Coalition for Democratic Change George Weah da na Jam'iyyar Unity mai mulki wato Joseph Boakai. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China