in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi nasarar kamalla zaben shugaban kasa a Liberia
2017-10-11 09:21:06 cri
Shugaban hukumar zabe na Liberia Jerome Korkoya, ya ce ba a samu rahoto wani gagarumin tashin hankali ba a lokacin da aka bude rumfunan zabe domin zaben sabon shugaban kasar.

Al'ummar kasar dake yammacin Afrika, sun shiga dogayen layuka a fadin kasar domin zaben mambobin majalisar wakilai 73.

Jerome Korkoya, ya ce an yi nasarar gudanar da babban zaben kasar lami lafiya, in ban da 'yar hatsaniya da aka samu daga bangaren masu kada kuri'a.

Ya shaidawa manema labarai a Monrovia babban birnin kasar cewa, rahoton farko-farko da hukumar ta tattara ya nuna cewa mutane da dama sun fita domin kada kuri'a.

Ya ce rahotanni sun nuna cewa komai ya tafi daidai cikin kwanciyar hankali kamar yadda aka tsara.

Jimilar 'yan takara 20 ne suka shiga zaben domin maye gurbin shugaba Ellen Johnson Sirleaf mai shekaru 78 da haihuwa da take gab da kammala wa'adin mulkinta na biyu. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China