Wata sanarwa da kungiyar ta fitar jiya, ta ruwaito cewa an nada tsohon shugaban kasar ne bisa la'akari da irin rawar da ya taka lokacin da yake jagorantar shugabannin kasashe mambobin kungiyar, ta fuskar wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin da ma nahiyar baki daya.
Tsohon shugaban kasar na Ghana, ya kasance jagoran wakilan kungiyar kasashe renon Ingila ta Common Wealth, da suka sa ido kan zaben kasar Kenya da aka yi a watan Augustan da ya gabata, haka zalika, ya jagoranci wakilan ECOWAS da suka shiga tsakani yayin rikicin mika mulkin kasar Gambia a farkon shekarar nna. (Fa'iza Mustapha)