in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya gana da firaministan kasar Canada
2017-12-05 20:37:31 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da firaministan kasar Canada Justin Trudeau a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

Yayin ganawar ta su a Talatar nan, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ce yadda ake kokarin musayar ra'ayi tsakanin shugabannin kasashen Sin da Canada, shi ne ya tabbatar da saurin ci gaban huldar dake tsakanin bangarorin 2. Ya ce tun da kasashen 2 suna iya taimakawa juna a fannoni daban daban, ya kamata su habaka hadin gwiwar dake tsakaninsu, tare da neman samun ci gaban hadin kansu a fannonin makamashi, da kirkiro sabbin fasahohi, da zirga-zirgar jiragen sama, da hada-hadar kudi, da aikin gona na zamani, da fasahohi marasa gurbata muhalli, da dai sauransu.

A nasa bangare, firaministan kasar Canada, Justin Trudeau ya ce, hadin gwiwar dake tsakanin Canada da Sin, ya samar da takamaimiyar moriya ga jama'ar kasashen 2. Don haka kasar Canada na fatan zurfafa dangantakar dake tsakaninta da kasar ta Sin, bisa tushen girmama juna, da amincewa da juna. Haka zalika, babban jami'in na kasar Canada ya bayyana burin kasarsa, na kara bunkasa mu'amala da hadin gwiwa da kasar Sin, musamman ma a fannonin tattalin arziki da cinikayya, da aikin ilimi, da kuma al'adu. Yana kuma fatan ganin kasashen Canada da Sin sun kara kokarin daidaita ra'ayoyinsu kan wasu manyan batutuwa masu muhimmanci, masu alaka da harkokin kasa da kasa, da ma na wasu yankuna.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China