A cewar wani daftarin ka'idoji da kotun kolin jama'a ta fitar a jiya, dole ne a matsa lamba wajen yaki da batutuwan kafa gidauniyar tara kudi ba bisa ka'ida ba ta intanet, wanda su ne jigo wajen takaita matsalolin kudi.
Domin magance irin wadanan batutuwa, daftarin ka'idojin ya ce ya kamata kotuna su hada hannu da hukumomin yankuna domin kare wadanda ka laifuffukan ka iya rutsawa da su.
Ka'idojin sun kuma bayyana batutuwan da suka shafi karbar kafin alkalami ba bisa ka'ida ba daga al'umma ko kuma kafa gidauniyar tara kudi da sunan asusun ajiya.
Sun kuma yi bayani game da yadda za a tafiyar da karar da ta shafi rikice-rikicen kudi.
Sama da mutane 16, 400 ne aka gurfanar da gaban kotu bisa laifuffuka daban-daban da suka shafi hada-hadar kudi a shekarar 2016. (Fa'iza Mustapha)