in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban bankin kasar Sin zai sakawar kasuwa mara a wannan shekara
2017-07-07 09:17:01 cri
Babban bankin al'umma na kasar Sin (PBOC) ya bayyana cewa, a wannan shekara, kasuwar hannayen jari za ta mayar da hankali kan yadda matakan gyare-gyare suka shafi harkokin kasuwar hada-hadar kudi

Wani rahoto da aka fitar game da ci gaban kasuwar hannayen jarin kasar ta Sin na shekarar 2016 da ta gabata, wanda babban kasar ta Sin ya wallafa a shafinsa na Intanet, ya nuna cewa, za a yayata gyaran fuskar da aka yi wa adadin kudaden ruwan da kasuwa ta yarda a karba.

Rahoton ya ce, za a inganta tsari da adadin kudin ruwa ne domin kara karfin babban bankin na daidaita batun irin wadannan kudade ruwa.

Bugu da kari, mahukuntan kasar Sin za su kara kyautata yadda babban bankin yake gudanar da ayyukansa, ciki har da matakan bayar da basussuka, da rance mai matsakaicin wa'adi da kuma sake bibiyar wannan rahoto a lokacin da bukatar hakan ta taso.

Rahoton ya kara da cewa, kasar Sin za ta kara inganta yadda ake musayar kudade a kasuwa, don kyautata darajar kudin kasar na RMB a kan dalar Amurka. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China