Wata sanarwar da hukumar kula da harkokin kudaden musayan ketare ta majalisar gudanarwar kasar ta fitar a yau Jumma'a, ta bayyana ceewa, daga ranar 1 ga watan Satumban wannan shekara, an bukaci bankuna da su rika bayar da rahoto game da kudaden da masu hulda da su suka cire da kuma duk wasu yarjejeniyoyin da aka kulla wadanda suka haura Yuan 1,000 da manyan shaguna, ko aka cire a ketare ta hanyar amfani da katunan cire kudade na bankuna.
Sanarwar ta ce, an dauki wannan mataki ne, domin inganta ayyukan bankunan da inganta muhimman bayanai game da kudaden da aka cire a ketare ta hanyar amfani da katunan bankuna ta yadda zai dace da bukatun hadin gwiwar kasa da kasa na yaki da halatta kudin haram, da katse kafofin da 'yan ta'adda ke samun kudade, da yaki da masu kin biyan haraji. (Ibrahim)