Kamfanin kera roka da zirga-zirgar sararin samaniya na kasar Rasha mai suna Energia wanda ya yi nasarar harba tauraron dan-Adam na kasar Angola zuwa sararin samaniya, ya ce an daina jin duriyar tauraron dan-Adam din a halin yanzu.
A ranar Talatar da ta gabata ce aka yi nasara harba tauraon dan-Adan din, da nufin watsa shirye-shiryen talabijin a kasar, amma bayan wani lokaci, sai sadarwa da shi ta katse.
A ranar 28 ga watan Nuwamban wannan shekara ce, kasar Rasha ta harba wani roka mai dauke da taurarin dan-Adam 19, amma kuma aka daina jin duriyarsu jim kadan bayan tashinsu zuwa sararin samaniya.
Da farko dai, an tabbatar da cewa, bangaren rokar dake dauke da taurarin dan-Adan din ya fada cikin teku. (Ibrahim)