in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jirgin ruwan kasar Sin mai bada agajin kiwon ya tallafawa mutane 6,000 a Angola
2017-10-27 11:44:13 cri

Jirgin ruwan kasar Sin mai bada agajin kiwon lafiya wato Peace Ark, ya yiwa majinyatan kasar Angola kimanin dubu 6 magani cikin kwanaki 8 da ya shafe a kasar.

Kwamandan kula da shirin Guan Bailin, ya bayyana jiya a Luanda babban birnin kasar cewa, a tsawon lokacin da suka shafe a kasar, sun gudanar da aikin tiyata kimanin 14.

Ya ce mafi yawan kwararrun da suka gudanar da aikin sun hada da masana cutukan ido, da na zuciya, da kuma kwararru a fannin kashi.

Kafin gudanar aikin a kasar Angola, Peace Ark ya ziyarci kasashen Djibouti, Gabon, Saliyo da Jamhuriyar Kongo. Daga bisani kuma zai zarce zuwa kasashen Mozambique da Tanzaniya.

Guan ya nanata cewa, manufar ziyarar jirgin ruwan ita ce, karfafa dangantakar dake tsakanin sojojin ruwa na Angolan da na Sin.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China