in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rantsar da sabon shugaban kasar Angola
2017-09-27 10:03:49 cri
A jiya Talata ne aka rantsar da Joao Lourenco a matsayin sabon shugaban kasar Angola, inda ya maye gurbin Jose Eduardo dos Santos wanda ya dade yana jan ragamar mulkin kasar.

Lourenco mai shekaru 63 wanda ya yi takara a babban zaben kasar na ranar 23 ga watan Agustan wannan shekara karkashin jam'iyyar MPLA mai mulkin kasar, ya samu kaso 61 cikin 100 na kuri'un da aka kada.

Daga cikin wadanda suka halarci bikin rantsar da sabon shugaban har da shugabannin kasashe da gwamnatoci kimanin 30 wadanda suka hada da kasashen Afirka ta kudu, da Guinea Bissau, da Equatorial Guinea, da Namibia, da Cote d I'Voire da Rwanda, da Portugal, da Zambia da Jamhuriyar Congo da Guinea da Gabon da Jamhuriyar Demokiradiyar Congo, da kuma Chen Yuan, manzon musamman na shugaba Xi Jinping na kasar Sin.

Kimanin mutane 1,000 daga ciki da wajen kasar ne suka halarci bikin rantsar da sabon shugaban, wanda aka gudanar a dandalin Jamhuriya dake Luanda, babban birnin kasar. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China