in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane a kalla 100 sun mutu yayin da wasu dubbai suka jikkata sanadiyyar girgizar kasa a iyakar Iraki da Iran
2017-11-13 10:45:18 cri
Mutane a kalla 100 ne suka mutu, yayin da wasu dubbai suka jikkata, sanadiyyar wata girgizar kasa mai karfin maki 7.2 da ta auku jiya Lahadi a yankin kan iyakar Iran da Iraki.

Girgizar ta auku ne kilomita 103 daga kudu maso gabashin birnin Sulaymaniyah ta Iraki, kuma an ji amonta a larduna da dama na Iran dake iyaka da Iraki.

Kungiyoyin bada agaji na Iran sun garzaya yankin da girgizar ta auku inda jirage masu saukar ungulu ke kai taimako ga mutanen da iftala'in ya aukawa. (Fa'iza Mustaphha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China