Yayin zantawa da manema labarai a jiya Alhamis, Geng Shuang ya ce suna kyautata fatan cewa, al'amura za su daidaita, sannan za a warware dukkan batutuwa cikin ruwan sanyi a kasar.
A ranar Laraba da ta gabata ne rundunar sojin kasar Zimbabwe ta sanar da karbe iko da gwamnatin kasar dake yankin kudancin Afrika, tare da yi wa shugaban kasar Robert Mugabe mai shekaru 93 da matarsa daurin talala tun da safiyar ranar.
Shugabannin rundunar sun bayyana ta gidan talabijin na kasar cewa, yunkurin nasu ba ya nufin juyin mulki, illa dai, suna farwa masu laifi dake zagaye da shugaban, inda suka ce Robert Mugabe da iyalansa na cikin koshin lafiya, suna masu bada tabbacin tsaronsa.
Da yake amsa tambaya game da jarin kasar Sin a Zimbabawe, Geng Shuang ya ce hadin gwiwa da amincin dake tsakanin kasashen biyu ta kunshi dukkan bangarori, kuma tana amfanar al'umomin kasashen. (Fa'iza Mustapha)