in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na shirin kammala tashar bincike ta 5 a yankin Antartika a 2022
2017-11-08 10:28:36 cri

Daraktan cibiyar binciken yankunan masu sanyi na kasar Sin Yang Huigen, ya ce kasar na shirin kammala tashar bincike ta 5 a yankin Antartika nan da shekaru 5 masu zuwa.

A yau Laraba ne jirgin ruwan dake shiga kankara na kasar Sin wato Xuelong zai bar birnin Shangahai, domin fara aikin bincike karo na 34, a yankin Antartika mai cike da kankara.

Babbar manufar binciken da ya kunshi mambobi 334 ita ce, fara gina sabuwar cibiyar bincike da za ta rika aiki kowane lokaci cikin shekara, a gabar tsibirin Terra Nova na tekun Ross.

Sabuwar cibiyar za ta cike gibin da kasar Sin ke da shi a fannin bincike a yankin Antartika, tun da tasoshin babbar ganuwa da Zhongshan sun mamaye sassan daban-daban, inda daya ke fuskantar tekun Atlantika yayin da dayan kuma ke fuskantar tekun Indiya.

Tekun Ross wanda ke fuskantar kudancin Fasifik na da yankin kankara mafi girma a nahiyar, kuma ana ganinsa a matsayin muhallin hallitun ruwa mai dimbin albarkatu da ba a gurbata ba.

Sabuwar tashar za ta kunshi kayayyakin kai daukin gaggawa, tare da cimma bukatun aiki da na lafiya da zaman rayuwar ma'aikata a kowane lokaci.

Za kuma a samar mata da kafar sadarwa ta tauraron dan Adam da lantarki da ruwa da na'urar dumama wuri da kayayyakin sufuri, ciki har da kananan jiragen sama da masu saukar ungulu. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China