in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta harba sabon tauraron dan Adam mai duba yanayi
2017-11-15 09:59:13 cri
Kasar Sin ta harba wani sabon tauraron dan Adam mai duba yanayi wato Fengyun-3D, da misalin karfe 2:35 na safiyar yau Laraba agogon Beijing, daga cibiyar harba tauraron dan Adam ta Taiyuan dake lardin Shanxi na arewacin kasar.

Linzamin Long March-4C ne ya harba tauraron zuwa sararin samaniya, inda ya fara zagaye.

Fengyun-3D na daya daga cikin na'urori sabbin kirkira dake duba yanayin yankuna masu sanyi, wanda ke samar da cikakkun bayanai dangane da yanayin sassan duniya masu cike da hotuna irin na zamani da ake bukata. Tauraron zai yi aiki tare da da tauraron Fengyun-3C wanda aka harba cikin watan Satumban 2013, domin fadada ayyukan tattara bayanai game da sararin samaniya, musammam yanayin iskar dake shafar rayuwar bil'adama. Matakin da zai taimakawa aikin kasar Sin na kai dauki yayin aukuwar annoba.

Kwalejin horas da fasahohin sararin samaniya ta Shanghai ce ta kirkiro tauraron Fengyun-3D da linzamin Long March-4C karkashin kulawar hukumar lura da kimiyya da fasahar da ta shafi sararin samaniya ta kasar Sin.

Harbin na wannan karon shi ne aiki na 254 cikin jerin ayyukan linzamin Long March. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China