in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da jirgin ruwan zamani kirar kasar Sin na farko a Shanghai
2017-12-06 10:42:16 cri
A jiya Talata aka kaddamar da jirgin ruwa na zamani kirar kasar Sin na farko wanda ke kunshe da na'urorin binciken cikin teku na zamani a birnin Shanghai.

Jirgin ruwan wanda ke da tsawon mita 179, yana iya yin binciken sirri, yana da fadin mita 32, kuma yana da tudun mita 15, zai iya daukar nauyin ton 38,800. Jirgin ruwan wanda aka kera shi bisa tsarin fasahar harkokin teku ta SOMS ta kasar Sin, yana kunshe da na'urorin bincike na zamani da kuma tsarin da zai iya sarrafa kansa. Haka zalika sabon samfurin jirgin ruwan zai iya samar da bayanai da bincike a cikin teku, zai iya zabar hanya mafi dacewa a cikin teku, kuma zai iya sanar da matukansa da zarar ya hangi wata barazana da za'a iya cin karo da ita.

Hukumar samar da jigaren ruwa ta kasar Sin (CSSC) ce ta kera jirgin ruwan, za'a yi amfani da sabon samfurin jirgin ruwan na zamani ne wajen takon sinadarin kwal da gishiri tsakanin kasar Sin da Australia da kuma kudu maso gabashin Asiya.

Ingancin jirgin ruwan ya kai matsayin koli, kuma tuni ya riga ya tsallake tantancewar hukumar tantancewa ta kasar Sin da hukumar rijistar jiragen ruwa ta Lloyd. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China