in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yada akidun kimiyya na samun karin karbuwa tsakanin al'ummar Sin
2017-11-28 10:44:21 cri

Ma'aikatar kimiyya da fasaha ta kasar Sin, ta bayyana irin ci gaban da aka samu, game da yaduwar ilimin kimiyya da fasaha tsakanin al'ummar Sinawa.

Domin cimma wannan buri, wata takardar bayani da ma'aikatar ta fitar ta ce, a bara, mahukuntan kasar sun samar da kudi da yawan su ya kai dalar Amurka biliyan 2.3, adadin da ya haura na shekarar bara 2015 da kaso 7.63 bisa dari domin bunkasa wannan fanni.

Takardar ta kara da cewa, ya zuwa karshen shekarar 2016, an kammala samar da cibiyoyi, da wuraren adana kayayyakin tarihi masu nasaba da harkokin kimiyya da fasaha, wadanda yawan su ya kai 1,400. Adadin da ya haura na shekarar da ta gabaci hakan da kaso 10.7 bisa dari.

Kaza lika yawan mutanen dake cikakken aiki a irin wadannan wurare a shekarar ta 2016 ya kai mutum 223,500, adadin da ya haura na shekarar 2015 da kusan mutum 2,000.

Da yake karin haske game da wannan batu, jami'i a sashen yayata manufofin kimiyya a ma'aikatar Qiu Chengli, ya ce bisa matsakaicin ma'auni, yawan mutanen dake amfana daga ayyukan cibiyar yayata manufar fasaha daya tak, ya kai mutane miliyan guda a shekarar ta bara.

Mr. Qiu ya kara da cewa, Sin za ta gina karin cibiyoyin bunkasa kimiyya da fasaha, da wuraren killace kayayyakin da suka jibanci hakan, a yankuna masu karancin ci gaba dake yammacin kasar, da yankunan kananan kabilu domin samar da daidaito na ci gaba a sashen.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China