in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar AU za ta aike da jami'an sa ido zuwa Liberia
2017-10-03 13:11:14 cri
Kungiyar tarayyar Afirka ta AU, na shirin aikewa da wata tawagar jami'ai, wadda za ta yi aikin sa ido na gajeren lokaci, game da shirin gudanar zabe a kasar Liberia.

Tuni dai AUn ta aike da jami'anta dake aikin lura da shirin zaben kasar mai dogon wa'adin aiki, gabanin zaben shugaban kasa da na 'yan majalissar Liberia dake tafe a ranar 10 ga watan Oktobar nan.

Wata sanarwa da hedkwatar hukumar ta fitar a ranar Litinin, ta ce shugaban hukumar gudanarwa kungiyar ta AU Moussa Faki Mahamat, ya amince da tura tawagar bisa gayyatar mahukuntan Liberia.

Tawagar jami'an dake shirin isa Liberia na kunshe ne da jami'ai 50, za kuma ta yi aikin ta kafada da kafada da wadda ke da dogon zango na wa'adin aiki, wadda tun ranar 1 ga watan Satumba ke kasar ta Liberia.

Tawagogin biyu dai na da nauyin lura, tare da tabbatar da ana kiyaye dokokin kasar ta Liberia masu alaka da zabe, da ma sauran dokoki na kasa da kasa.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China