in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta goyi bayan yarjejeniyar tsakaita bude wuta a jamhuriyar Kongo
2017-12-27 09:53:46 cri
Sakatare janar na MDD Antonio Guterres, ya goyi bayan yarjejeniyar tsakaita bude wuta da aka rattaba hannu kanta a ranar Asabar, tsakanin gwamnatin jamhuriya Kongo da kungiyar 'yan tawayen kasar karkashin jagorancin Pastor Ntumi.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun babban sakataren MDD Stephane Dujarric ya fitar ya bayyana cewa, Guterres ya bayyana kyakkyawar fata cewa, wannan yarjejeniya za ta share fagen samun dawwamammen zaman lafiya da kuma cimma matsaya wajen warware rikicin da ya kaure a yankin Pool na kasar, kuma zai kawo karshen rashin tabbas da masu bukatar agaji ke fuskanta a yankin. Shi dai yankin na Pool, yanki ne mai arzikin mai dake kudancin jamhuriyar Kongo wanda ya hada har da Brazzaville, babban birnin kasar.

Dujarric ya ce, MDD a shirye take ta goyi bayan bangarorin biyu wajen aiwatar da yarjejeniyar tabbatar da zaman lafiyar.

Tashin hankali ya kaure ne a kasar ta tsakiyar Afrika, tun bayan da shugaban kasar Denis Sassou Nguesso, ya lashe zaben shugabancin kasar da aka gudanar a watan Aprilun shekarar 2016. Gwamnatin kasar ta zargi Ntumi da laifin amfani da mayakan kungiyar 'yan adawar wajen kaddamar da munanan hare-hare kan jami'an 'yan sanda, da barikokin soji da kuma gine-ginen gwamnati. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China