in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhu na MDD ya gargadi game da jinkirta zabe a DRC
2017-11-29 10:44:54 cri
Kwamitin sulhu na MDD ya yi maraba da wallafa jadawalin zabe a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo, yana mai gargadi game da duk wani nau'in yunkuri na jinkirta zaben.

Sanarwar da majalisar ta fitar jiya ta ce, Majalisar ta lura da ranar 23 ga watan Disamba na shekarar 2018 da aka wallafa a matsayin ranar gudanar da zaben shugaban kasa da na majalisun dokoki da na larduna.

Kwamitin ya jadadda cewa, sahihin zabe cikin kwanciyar hankali na da muhimmanci matuka wajen tabbatar da dorewar zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar.

Ya kuma yi kira ga hukumomin kasar da sauran hukumomi masu ruwa da tsaki, su dauki dukkan matakan da suka wajaba ba tare da bata lokaci ba, domin tabbatar da kiyaye sabon lokacin zaben, ciki har da wallafa sahihin kasafin kudi domin zabukan da kuma zartar da dokokin zabe da suka dace.

Har ila yau, ya jadadda bukatar yin dukkan mai yuwa wajen ganin an shirya zaben bisa sharuda na gaskiya da sahihanci da za su kai ga mika mulki cikin ruwan sanyi.

Kwamitin sulhu ya kuma kara da rokon dukkan al'ummar kasar su yi aiki tare wajen ganin an alkinta jalli-jogan nasarorin da aka samu na zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar. Yana mai kira ga dukkan jam'iyyun siyasa da magoya bayansu da sauran masu ruwa da tsaki cikin harkar, su kwantar da hankalinsu, su kauracewa duk wani salon rikici. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China