in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban jami'in MDD zai ziyarci jami'an wanzar da zaman lafiya a CAR
2017-10-19 09:41:50 cri
A mako mai zuwa ne sakatare janar na MDD Antonio Guterres zai ziyarci jamhuriyar tsakiyar Afrika CAR, domin jinjinawa jami'an wanzar da zaman lafiya dake gudanar da aiki a kasar.

Guterres zai halarci bikin ranar MDD wanda za'a gudanar a ranar 24 ga watan Oktoba, tare da tawagar dakarun wanzar da zaman lafiyar na MDD dake aiki a CAR, domin nuna yabo da irin rawar da suke takawa wajen tabbatar da zaman lafiya da kuma bincike game da zarge-zargen aikata fyade da ake zargin wasu daga cikin dakarun wanzar da zaman lafiyar da hannu cikinsa.

Jami'in MDD ya shedawa 'yan jaridu cewa, aikin wanzar da zaman lafiya yana daga cikin manyan hanyoyin da kasa da kasa ke amfani da su wajen magance kalubalolin tsaro da zaman lafiya dake addabar duniya. Dakarun wanzar da zaman lafiya suna yin aiki tukuru wajen ba da gudunmawa a yankunan da ake fama da tashe-tashen hankula, kuma aikin ya kasance wani muhimmin sadaukar da kai wajen taimakawa kasashen duniya da suke fuskantar matsalolin kungiyoyi masu dauke da makamai.

Guterres, ya kuma danganta ziyarar tasa da batutuwa da suka shafi cin zarafin da ke da haddin jama'a da ake zargin jami'an da aikatawa. Ya ce sabon tsarin da aka bullo da shi na magance wannan matsalar yana samun goyon baya yadda ya kamata. Ya ce kimanin kasashen duniya 72 ne suka rattaba hannu kan wannan batu, kuma kasashe 19 daga cikinsu sun nuna tsananin bukatarsu na aiwatar da wannan shiri, kana shugabannin kasashe 57 sun riga sun shiga cikin shirin na yaki da cin zarafi da aikata fyade. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China