in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi Allah wadai da kashe jami'an kiyaye zaman lafiya a CAR
2017-12-05 11:00:46 cri
Sakatare janar na MDD Antonio Guterres, ya yi Allah wadai da harin da aka kaddamar kan jami'an 'yan sandan masu binciken ababen hawa a jamhuriyar tsakiyar Afrika CAR, wanda ya yi sanadiyyar hallaka jami'in kiyaye zaman lafiya guda da kuma jikkata wasu jami'an 3.

Mai magana da yawun sakataren MDD Stephane Dujarric, ya bayyana cewa a lokacin harin na ranar Litinin wanda mayakan kungiyar anti-Balaka suka kaddamnar a Bria, babban birnin jahar Haute-Kotto, an kashe wani jami'in kiyaye zaman lafiya guda dan kasar Mauritania, kana an jikkata wasu jami'an 3, da suka hada da 'yan kasar Mauritania 2, da kuma guda dan kasar Zambia.

Mista Guterres, ya yi Allah wadai da kaddamar da harin, kana ya aike da sakon ta'aziyya ga gwamnati da al'ummar kasar Mauritania da kuma abokan aikinsu na rundunar wanzar zaman lafiya ta MDDr. Kana ya yi fatan samun sauki cikin hanzari ga wadanda suka jikkata a sanadiyyar harin.

Kakakin MDD ya ce, harin ya zo ne sa'o'i biyu bayan da jami'an kiyaye zaman lafiyar suka yi kokarin ceto wasu mutane biyu da mayakan anti-Balaka suka yi garkuwa da su a Bria.

CAR ta fada yakin basasa ne tun a shekarar 2012, sakamakon barkewar tashin hankali wanda ke da nasaba da rikicin addini da na kabilanci, tsakanin mayakan Kiristoci na anti-Balaka da mayakan musulmi na Seleka. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China