A jiya ne kasar Morocco ta yi nasarar harba wani tauraron dan Adam mai aikin sanya ido zuwa sararin samaniya.
Tauraron dan Adam din mai suna Mohammed VI-A, wanda aka harba shi daga cibiyar zirga-zirgar sararin samaniya ta French Guiana da misalin karfe 1 da mintuna 42 agogon GMT, za a yi amfani da shi ne wajen ayyukan tsarawa da kuma yin safiyo, da ayyukan raya yankuna, aikin gona, da rigakafin aukuwar bala'u. Sauran sun hada da canje-canjen da ake samu a fannonin muhalli da kwararowar hamada, da kuma sanya ido a kan iyakokin kasa da na ruwa.(Ibrahim)