Taron zai ja hankalin manyan 'yan kasuwar nahiyar da na kasar Sin sama da 400, inda za a tattauna hanyoyin saukaka kasuwanci tsakanin manyan masu ruwa da tsaki kan harkokin cinikayya da zuba jari tsakanin kasar Sin da kasashen Arfika domin kyautata hadin gwiwa a tsakaninsu musammam a bangaren masana'antu.
Sanarwar da mashirya taron suka fitar, ta ce taron da za a shafe yini 2 ana yi zai tattauna tare da muhawara kan matsalolin kudi ga tattalin arzikin Afrika da kuma yadda za a mayar da nahiyar wani dandali na raya ayyukkan masana'antu.
Baya ga taron, za kuma a gudanar da wani taron bitar da zai bada damar fahimtar manufofin tattalin arzikin kasar Sin da na Afrika tare da yanayin gudanar da ayyuka.
Kasar Sin ita ce muhimmiyar abokiyar huldar kasuwanci ga nahiyar Afrika, inda ta zuba da sama da dala biliyan 122 cikin harkokin cinikayya tare da jarin kai tsaye da ba na ruwan kudi ba da ya kai dala biliyan 2.5 a nahiyar (Fa'iza Mustapha)