in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan mutanen da suka rasu sakamakon farmakin ta'addanci a Masar ya karu zuwa 305
2017-11-26 13:56:41 cri
Babban mai gabatar da kara a kotun kasar Masar ya bayar da sanarwa a jiya ranar Asabar cewa, ya zuwa yanzu, harin ta'addancin da aka kai a wani masallacin kasar ya hadassa rasuwar mutane a kalla 305, tare kuma da rautata mutane 128. Wadanda suka kaddamar da harin suna rike da tutar kungiyar IS.

Masallacin na da tsawon kilomita 40 a yammacin Al-Arish, hedkwatar lardin arewacin birnin Sinai. Lamarin ya faru ne a yayin mutane masu yawa dake halartar masallacin don gabatar da salla.

Sanarwar ta ce, yawan 'yan ta'addan da suka kaddamar da harin, ya kai 25 zuwa 30, bayan da suka isa masallacin cikin wasu manyan motoci masu manyan tayu biyar, sai suka fara jefa boma-bomai sannan suka fara yin harbe harbe cikin masallacin. A lokaci guda kuma, suna kada tutar mai alamar IS. Baya ga haka, sun kona wasu motocin dake kewayen masallacin bayan farmaki, daga bisani suka tsere daga wajen.

Har zuwa yanzu, babu wata kungiyar da ta sanar da daukar alhakin farmakin.

Bayan aukuwar lamarin, bangaren gwamnatin Masar ya sanar da cewa, an ware kwanaki 3 don zaman makoki a duk fadin kasar wanda aka fara tun daga ranar 24 ga wata. A ranar 25 ga wata kuma, shugaba Abdel-Fattah al-Sisi na kasar ya bada umurnin gina wani abu na tunawa da wadanda suka rasa rayukansu sakamakon farmakin. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China