A cewar sanarwar da AU ta fitar jiya, taken taron da aka fara daga Alhamis zuwa yau Asabar, shi ne "mara baya ga samar da dabarun tabbatar da zaman lafiya domin yankunan da rikicin Boko Haram ya shafa."
Dabarar tabbatar da zaman lafiya a yankin shi ne matakin farko na samar da cikakken tsarin tabbatar da kwanciyar hankali a yankin, wanda zai samar da shirye-shirye da dama dake da nufin tabbatar da tsaro a yankunan da rikicin Boko Haram ya shafa.
Shugaban kwamitin sulhu na AU Smail Chergui da minsitan ruwa da tsaftar muhalli na Chadi Sidick Abdelkeria Haggar da kuma sakataren zartaswa na hukumar kula da yankin tafkin Chadi Engr Sanusi Imran Abdullahi ne suka jagoranci bikin bude taron.
Mahalarta taron sun hada da wakilan wadanda hare-haren Boko Haram ya rutsa da su da kungiyoyin al'umma daga yankunan da rikicin ya shafa da gwamnoni da masu sarauta da jami'ai daga kasashen yankin tafkin Chadi da Benin da Au da wakilan MDD da na hukumominta dake aiki a yankunan da kuma sauran hukumomin kasashen ketare. (Fa'iza Mustapha)