in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan Boko Haram sun fille kan manoma 6 a arewa maso gabashin Najeriya
2017-11-21 12:41:11 cri
Wasu da ake zargin mayakan 'yan ta'adda na Boko Haram ne sun fille kan wasu manoma su 6 a wani kauye dake jahar Borno a arewa maso gabashin Najeriya.

Wata majiya ta ambata cewa, lamarin ya afku ne a ranar Lahadi a dajin Dimge dake karamar hukumar Mafa ta jahar Borno.

Usman Muhammed, mamba ne a rundunar tabbatar da tsaro masu aikin sa kai, ya shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, 'yan ta'addan sun yiwa yankin dirar mikiya ne akan Babura. Wadanda aka hallaka din suna aiki ne a cikin gonakinsu.

Sai dai kawo yanzu hukumomin tsaron Najeriya basu tabbatar da faruwar al'amarin ba.

Ana zargin kungiyar Boko Haram da hallaka mutane sama da dubu 20 da kuma raba mutane miliyan 2 da dubu 300 da muhallansu a Najeriyar tun bayan fara kaddamar da hare haren kungiyar a shekarar 2009.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China