in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya aika da sakon taya murnar budewar taron tattaunawar fasahohin yanar gizo na Internet
2017-12-03 16:42:43 cri
A yau Lahadi, aka bude taron tattaunawar fasahohin yanar gizo ta Internet na kasa da kasa karo na 4 a birnin Wuzhen na lardin Zhejiang dake gabashin kasar Sin, inda shugaban kasar Xi Jinping ya aike da sakon taya murnar bude taron. A cikin sakon da ya aike da shi, shugaba Xi ya nuna matukar farin cikinsa kan bude taron.

Shugaban ya fada a cikin sakonsa cewa, a wajen taron wakilan jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin karo na 19 da ya kammala a watan Oktoban bana, an tabbatar da manufofin da kasar za ta dauka don biyan bukatun raya tsarin mulki na gurguzu mai halayyar musamman ta kasar Sin a sabon zamanin da ake ciki, matakan da suka kunshi raya fasahohin yanar gizo ta Internet, da yada fasahohin zamani masu alaka da harkar sadarwa, da kirkiro mutum-mutumi na zamani da ake kira Robot, da dai sauransu, don samun damar sa kaimi ga ci gaban tattalin arzikin kasar.

A cewar shugaban, bisa yanayin da kasar Sin ke ciki na kokarin raya tattalin arziki mai alaka da fasahohin sadarwa na zamani, kasar na fatan taimakawa sauran kasashe domin su ma su samu ci gaba a wannan fanni. A nata bangare, kasar Sin ta yi alkawarin kara bude kofarta, maimakon rufe ta.

Zaunannen mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, Wang Huning, ya halarci bikin bude taron tattaunawar fasahohin yanar gizo ta Internet na kasa da kasa, inda ya gabatar da wani jawabi. A cewarsa, sakon taya murnar da shugaba Xi Jinping ya aika, ya nuna yadda shugaban yake da idon basira kan yanayin ci gaban fasahohi masu alaka da yanar gizo ta Internet a duniya, da ka'idojin da ake bi ta fuskar kula da yanar gizo ta Internet, haka zalika ya nuna yadda kasar Sin take son hadin gwiwa da sauran kasashe don neman ciyar da fasahohi masu alaka da Internet gaba. Kasar ta Sin za ta dora cikakken muhimmanci kan harkar raya yanar gizo ta Internet, kuma za ta yi hadin gwiwa tare da kasashe daban daban na duniya don tabbatar da ganin kowa ya amfana da cigaban fasahohin yanar gizo ta Internet.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China