Xi wanda ya bayyana hakan yayin da yake jawabi a bikin bude taron tattaunawa na JKS da sauran jam'iyyun siyasa na duniya da ya gudana a nan birnin Beijing, ya kuma nanata kudurin JKS na ci gaba da inganta rayuwar Sinawa da ma bil-Adam baki daya.
Ya ce, baya ga sauke nauyin dake wuyanta, JKS za ta kara samar da damammaki ga duniya ta hanyar kara raya kasar ta Sin.
Babban sakataren kwamitin koli na JKS ya kuma bayyana cewa, yanzu haka manufar nan ta gina al'umma mai kyakkyawar makoma bai daya ya fara aiki a zahiri, bisa ga yadda ake aiwatar da shwarar nan ta ziri daya da hanya daya, wadda ta kasance wata kafar hadin gwiwa tsakanin kasashen da abin ya shafa wajen cimma manufarsu ta samun ci gaba.
Shugaban ya kuma kara da cewa, jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin(JKS) ba za ta shigo da wasu bakin tsare-tsare na samun ci gaban kasa ba, haka kuma ba za ta fitar da nata tsare-tsaren ko kuma ta tilastawa wata kasa ta kwaikwayi nata tsarin ba. (Ibrahim)