Ministan albarkatun man fetur na Najeriya Ibe Kachikwu, ya ce a mako mai zuwa ne gwamnatin kasar za ta sanar da keta hukumar albarkatun man kasar zuwa bangarori.
Mista Kachikwu ya fadawa manema labarai a Abuja cewar, za'a rarraba hukumar albarkatun man kasar wato NNPC ne zuwa kashi hudu ko biyar, kuma babban sashen gudanarwa na hukumar zai kunshi kamfanoni 30 wadanda zasu kasance karkashin daraktoci.
Ya kara da cewar ana gudanar da wasu muhimman ayyuka da zasu kawo sauye sauye masu yawa a sha'anin kamfanin man fetur na kasar, wanda ba'a taba gudanar da irinsa ba sama da shekaru 20 da suka gabata.
A cewar ministan, wadannan kamfanoni 30, muhimman ayyukansu shi ne lura da yadda aikin tafiyar da hada hadar albarkatun man kasar za ta gudana.
Najeriya ce kasar da ta fi arzikin man fetur a nahiyar Afrika, amma hukumar na fuskantar koma baya, sakamakon faduwar darajar danyen mai a kasuwannin duniya.(Ahmad Fagam)