Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, ya rattaba hannu kan kudurin kafa jami'ar nazarin harkokin man fetur, wadda za ta zama irinta ta farko a nahiyar Afrika.
Jami'ar za ta samu mazauni ne a jihar Delta dake yankin kudancin kasar, inda za ta mai da hankali kan darrusan injiniya da fasahohi da suka jibanci man fetur.
Nijeriya ita ce kasar da ta fi kowace samar da man fetur a Afrika, kuma ta kasance ta 6 a duniya. (Fa'iza Mustapha)