Mai magaba da yawun fadar ta White House Sean Spicer, ya bayyana cewa idan akwai wata hanya da Amurkar zata kawar da kungiyar ISIS zata yi hakan, ko ta hanyar hada kai da Rasha koma da wace irin kasar ce a duniya, domin tabbatar da tsaron Amurkar tabbas, a shirye Amurka take ta gudanar da wannan aiki.
Hakan na nufin matsayar da gwamnatin Amurka data shude ta dauka game da kin amincewa da hadin gwiwa da Rasha wajen kaddamar da hare hare ta sama a Syria ta kare.
Wannan jawabi ya zo ne bayan wata sanarwa da ma'aikatar tsaron Rasha ta fitar game da wasu jiragen yaki na hadin gwiwa da Amurka ta tura don kaddamar da hare hare ta sama tare da jiragen saman yakin kasar Rasha.
Sai dai fadar tsaron Amurka ta Pentagon ta musanta wannan rahoto.(Ahmad Fagam)