in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bankin Duniya zai tallafawa kasafin kudin Ghana na 2018 da dala miliyan 200
2017-12-22 10:09:05 cri

Gwamnatin kasar Ghana, ta ce Bankin duniya zai samar da dala miliyan 200 domin tallafawa kasafin kudin kasar na 2018.

Sanarwar da aka fitar jiya a birnin Accra, ta ce Bankin da Gwamnatin kasar sun rattaba hannu kan yarjejeniyar karbar rancen ne karkashin shirin na 2 na Gwamnati kasar, dake da nufin samar da kudi don bunkasa dukkan fannonin tattalin arziki da inganta karfin samar da aikin yi da kuma kula da matalauta da masu rauni.

Kafin rattaba hannu kan yarjejeniyar, kwamitin gudanarwar Bankin Duniya ya amince da samar da kudin ne yayin wani taro da ya gudana ranar Larabar da ta gabata a birnin Washington.

Sanarwar da aka fitar ta kara da cewa, shirin ya dace da kudurin Gwamnati mai ci, na ci gaba da tabbatar da daidaituwar harkokin tattalin arziki cikin matsakaicin lokaci, inda zai mai da hankali sosai kan matakan shari'a da manufofi na bai daya da za su zarce batun siyasa.

Ta kara da cewa, nasarar shirin na da muhimmanci ga daidaituwar dukkan fannonin tattalin arziki, wanda ake bukata don samun dorewar ci gaba. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China