Ministan ya ce akwai bukatar jajirtattun jami'ai su kasance cikin shiri, la'akari da yadda ake samun sauye-sauyen barazanar tsaro a duniya da kuma yadda bukatar masu shiga tsakanin na ketare ke kara karuwa yayin da ake rikici.
Da yake jawabi ga manema labarai a birnin Accra, Dominic Nitiwul ya ce kawo yanzu, dakarun kasar sun nuna juriya da kwarewa da kwazo da kuma karfin tunkarar duk wata barazana, ya na mai watsi da tsokacin da ake cewa, kashe kudi kan rundunonin soji banza ce,domin ana zaman lafiya a kasar. (Fa'iza Mustapha)