in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Daruruwan 'yan gudun hijirar Togo ne suka isa Ghana
2017-10-28 13:52:55 cri

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD UHNCR, ta ce sama da 'yan gudun hijira 500 da suka tserewa rikicin da ake a Jamhuriyar Togo ne suka isa Ghana.

Wata sanarwa da hukumar ta fitar jiya Jumma'a, ta ce hukumar na aiki da hukumomin kasar Ghana domin tallafawa 'yan gudun hijirar da suka tserewa tashin hankalin siyasa a Togo.

Rahotanni sun ce sojoji a kasar ta Togo na tafarwa 'yan adawa masu zanga-zanagar nuna kin amincewa da niyyar da ake zargin shugaban kasar Faure Gnassingbe na da ita, ta tsawaita wa'adin mulkinsa ta hanyar yi wa kundin tsarin mulkin kasar gyaran fuska.

Sanarwar ta ce mazauna yankunan kasar Ghana ne suka karbi galibin 'yan gudun hijirar, yayin da sauran ke wasu cibiyoyin al'umma.

Shirin kai dauki na hadin gwiwa tsakanin hukumar UNHCR da takwararta ta kasar Ghana, na kokarin isa yankunan domin tantance yanayin.

Jama'ar na Togo dake neman mafaka da suka hada da yara da mata, sun shaidawa hukumar UNHCR cewa, da kafa suka tsere, inda suka baro gidajensu dake yankin Mango na Togo, wanda ke kan iyakar kasar da Ghana.

Sun kara da cewa sun tsere ne domin gujewa musgunawa da ka iya biyo bayan rikicin siyasa da ta barke a baya-bayan nan

Sanarwar ta ce yanzu haka, Gwamnatin Ghana da hukumomin yankuna da al'ummomin da suka karbi bakin na samar musu da agajin gaggawa ciki har da abinci da wasu kayayyaki. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China