in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ghana ta kaddamar da shirin yaki da nuna bambanci tsakanin jinsi
2017-11-26 14:03:43 cri
A ranar Asabar kasar Ghana ta fara wani gangamin yaki da nuna bambanci tsakanin jinsi na cikin gida.

Shirin gwagwarmayar yaki da cin zarafin jinsin na kwanaki 16, ana shirya shi ne a duk shekara a fadin duniya daga ranar 25 ga watan Nuwambar kowace shekara a matsayin ranar yaki da cin zarafin mata ta kasa da kasa, har zuwa ranar 10 ga watan Disamba ne ake gudanar da bikin ranar 'yancin adam ta duniya.

Shirin gangamin ya bukaci gwamnatoci, da hukumomin kasa da kasa, da kuma kungiyoyin fararen hula da su kawar da duk wani tsari dake haifar da rashin daidaito da nuna wariya wanda yake shafar mata da 'yan mata da kuma mutanen da basu da galihu a tsakanin al'umma.

Ministar kula da harkokin mata da bada kariya ga kananan yara ta kasar Ghana, Otiko Afisah Djaba, ta bayyana cikin wata sanarwa cewa, wannan gangami zai ci gaba har zuwa lokacin da za'a kawo karshen cin zarafi da nuna wariya tsakanin jinsi a cikin gida, musamman ga mata da 'yan mata a duniya baki daya.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China