Akufo-Addo ya ce, gwamnatin da ta shude ta yi iyakar kokarinta wajen cusawa jama'a dabi'ar tsabtar muhallin da suke rayuwa cikinsa, sai dai bata kai ga yin nasara ba. Don haka ya ce gwamnatinsa ta lashi takobin bullo da sabbin dabarun cimma wannan buri.
Domin buga misali, shugaban na Ghana ya ce an tanadi jami'ai biyu a dukkannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin kasar wadanda za su dinga sa ido don ganin an mutunta dokar tsabtace dukkan ofisoshin gwamnati a kasar.
Bugu da kari, akwai wasu kungiyoyin matasa masu rajin tabbatar da tsabtar muhalli su ma za su sanya ido don ganin ana mutunta dokar tsabatar muhallin a dukkan ma'aikatun gwamnati da hukumomi masu zaman kansu har ma da gidajen alumma. (Ahmad)