An dai sanar da sunan 'yan wasan ne a jiya Litinin a birnin Accra na kasar Ghana, wato Mohamed Salah, da Sadio Mané da kuma Pierre-Emerick Aubameyang.
Ya zuwa yanzu a wannan kaka, Salah, dan wasan kungiyar Liverpool ya riga ya ciwa kungiyar sa kwallaye 14, kuma shi ne ke kan gaba a matsayi na farko a fannin cin kwallo a yanzu. Kana ya taimakawa kungiyar ta Liverpool sake shiga kungiyoyi 16 da ke buga gasar zakarun Turai bayan shekaru 9.
Salah, ya taimakawa kungiyar wasan kwallon kafa ta kasarsa ta Masar, samun damar shiga gasar cin kofin duniya bayan shekaru 28. Masu sha'awar kwallon kafa ta kasar Masar na kallon sa a matsayin jarumin kasar.
A daya hannun kuma Mané, shi ma dan wasan kungiyar Liverpool, ya na da kwarewa, ya kuma taka rawar gani a wannan shekara ta 2017. Ya zura kwallaye da dama a wasannin da kungiyarsa ta buga, kana ya jagoranci kungiyar wasan kwallon kafa ta kasarsa wato Senegal, inda ta kai ga sake shiga gasar cin kofin duniya bayan shekaru 16.
Aubameyang, dan wasan kungiyar Borussia Dortmund ta kasar Jamus ne, ya kuma taba samun lambar yabo ta dan wasan kwallon kafa mafi kwarewa na nahiyar Afirka a shekarar 2015. A wannan shekara, ya sake shiga takarar, saboda kwarewar da ya nuna a wasannin da kungiyarsa ta taka.
Za a gudanar da bikin bayar da lambobin yabo na hukumar hadin gwiwa ta wasan kwallon kafar Afirka, a ranar 4 ga watan Janairu na shekarar 2018, inda za a bayar da lambobi daban daban, baya ga ta dan wasan kwallon kafa mafi kwarewa a shekarar ta 2017. (Zainab)