Dan wasan wanda ke kan gaba a jerin mafiya ciwa kungiyar ta Arsenal kwallaye a tarihi, inda ya ci wa kungiyar kwallo har 228, ya yi kiran ne a ranar Litinin a birnin ikkon jihar Lagos, cibiyar kasuwancin Najeriyar.
Hukumar kare hadurra ta kasar FRSC ce dai ta gayyaci Herry, zuwa gangamin ta na wayar da kan direbobi, a gabar da aka fara tafiye tafiye na karshen shekara.
Henry ya ce yayi farin cikin sauka a Najeriya, ya kuma gane wa idanun sa hakikanin yadda kasar take. Ya ce "bisa abun da nake ta ji game da kasar, na gamsu da irin goyon bayan ta ga kwallon kafa. Ina matukar farin cikin zuwa Najeriya
Dan wasan ya kara da cewa, ya yi sa'ar taka leda da wasu taurarin kwallon kafa 'yan asalin Najeriya kamar Nwankwo Kanu, da Victor Ikpeba; wadanda dukkanin su sun bayyana masa kyawun Najeriya.
"Sun ce min al'ummar wannan kasa suna da matukar son kwallon kafa, kuma yanzu na ga hakan da idanu na, lallai na shaida hakan," a kalaman Herry.
Daga nana sai ya sake jan hankalin direbobin mota da su kaucewa tuki cikin maye, ko karya dokokin tuka.
Henry ya isa Najeriya a wani bangare na kewayen wayar da kan al'umma da kamfanin Guinness ya shirya, da hadin gwiwar hukumar kare hadurra ta Najeriya da kungiyar direbobin motocin haya ta kasar.(Saminu Alhassan)