Tsohon dan wasan na kulob din AC Milan, kana dan wasan tsakiya na kulob din Real Madrid, ya bayyana aniyarsa ta yin murabus din ne a shafukan sada zumunta na zamani, sama da watanni biyu bayan da ya buga wasansa na karshe a kungiyar wasan Orlando City.
"Abinda ban taba tsammani bane" Kaka ya rubuta a shafukan sada zumunta. "Na gode muku! "Yanzu na shirya tsab zan kara zuwa mataki na gaba."
Kaka ya taka leda ga kasarsa sau 95, ya kasance daga cikin tawagar 'yan wasan da suka taka rawa a nasarar cin kofin duniyar da Brazil ta samu a shekarar 2002, kuma an zabeshi zakaran 'yan wasan kwallon kafa na duniya a shekarar 2007.
Ya fara buga wasa ne da kulob din Sao Paulo a shekarar 2001, amma kuma yana tare da kulob din AC Milan wanda ya fara aiki dashi a shekarar 2003, a inda a kungiyar wasan ne ya samu maki mafi yawa.
A shekaru 6 da ya shafe yana murza leda, ya jagoranci wasanni a kungiyoyin wasan kwallon kafa na Italiya Scudetto tsakanin 2003 zuwa 2004, da Supercoppa ta Italiyan a 2004, sai kofin Super Cup 2007 UEFA, dana kofin duniya na FIFA a 2007, da kuma na Champions League a 2006 zuwa 2007.
Kaka ya koma zuwa Real Madrid a shekarar 2009 a kan kudi euro miliyan 67, koda yake, bai kai irin matsayi wanda ya samu a shekarun da ya shafe tare da Milan ba, ya taimakawa kulob din Spaniya a wasan Copa del Rey a shekarun 2010 zuwa 2011 La Liga a 2011 zuwa 2012.
Dan wasan, ya koma zuwa Milan a kakar wasanni ta 2013 zuwa 2014, kuma ya ci moriyar wasannin na tsawon watanni 5 tare da Sao Paulo kafin ya karkare wasansa na karshe da kungiyar wasa ta Orlando City.(Ahmad Fagam)