in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ghana ta rasa gurbin buga gasar cin kofin duniya na badi
2017-11-15 17:46:07 cri
Ghana ta rasa gurbin buga gasar cin kofin duniya na badi

Kasar Ghana ta yi rashin nasara, game da burin ta na buga gasar cin kofin duniya ta badi da za a fafata a Rasha, bayan da ta tashi wasan ranar Lahadin karshen mako da ci 1-1 ita da Masar.

Tun da fari dai dan wasan Masar Mahmoud Shikabala ne ya fara ciwa kungiyar kasar sa kwallo cikin minti na 61 da take wasa. Sai dai ba da dadewa ba cikin minti na 64, dan wasan Ghana Edwin Gyasi ya farke kwallon da Masar din ta zura masu.

Duk da irin matsin lamba da 'yan wasan Black Stars na Ghana suka yiwa Masar, bayan dawowa daga hutun rabin lokaci hakar su ta kara wa Masar din kwallo a raga ba ta cimma ruwa ba. Haka aka tashi wasan 1 da 1. Kuma da wannan sakamako, Ghana ta rasa gurbin ta na shiga a dama da ita a gasar ta badi, wadda za a buga a Rasha bisa jimillar kwallaye da Masar din ke da su sama da Black Stars.

Dama dai tun kafin wasan kungiyar Masar da ke rike da kofunan nahiyar Afirka har karo 7, ta riga ta samu gurbin buga gasar ta FIFA daga rukunin E, lamarin da ya dakile damar Ghana a rukunin, ta kasancewa wadda za ta halarci gasar ta duniya karo na 4 a jere.

Rabon da Masar ta kai ga buga kasar cin kofin duniyar dai tun a shekarar 1990.

Kafin wasan na karshen mako dai 'yan wasan Black Stars na Ghana sun sha alwashin lallasa Masar, sai dai 'yan wasan Masar din sun kai ga nasarar dakile aukuwar hakan, matakin da ya zama abun alfaharin ga Masar, wadda a irin wannan wasa da suka buga karon karshe a shekarar 2014, ta sha kasha hannu Ghana da ci 6-1.

Dukkanin sassan biyu dai sun buga wasan na karshen mako ba tare da manyan 'yan wasan su ba. Kocin Ghana Kwesi Appiah ya shiga wasan ba tare da Asamoah Gyan da Christian Atsu ba. 'yan wasan biyu sun ji rauni ne gabanin buga wasan na karshen mako

A wani ci gaban kuma kocin na Black Stars Kwesi Appiah, ya ce yanzu hankalin sa ya karkata ga lashe gasar nahiyar Afirka ta (AFCON), wadda ke tafe a shekarar 2019 a kasar Kamaru, shekaru 35 tun bayan daukar kofin a karon karshe.

"Mun san mun rasa damar buga gasar cin kofin duniya mai zuwa, don haka zan baiwa 'yan wasan mu damar nuna bajimtar su a shekarar 2019, a yayin gasar cin kofin Afirka" a kalaman koci Appiah yayin wani taron manema labarai.

A wasannin neman gurbin da aka kammala dai Black Stars ce ta 3 a rukunin E da maki 7, kasa da kungiyoyin dake gaban ta wato Masar da kuma Uganda.

Za dai a fidda jadawalin yadda gasar cin kofin duniya ta Rasha za ta gudana, a fadar Kremlin dake birnin Moscow, a ranar 1 ga watan Disambar dake tafe.

Croatia ta samu gurmin buga gasar cin kofin duniya na Rasha

Kasar Croatia ta yi nasarar samun gurbin buga gasar cin kofin duniya ta kwallon kafa wadda hukumar FIFA ke shirya, wadda kuma za a buga badi a kasar Rasha. Croatia ta samu wannan nasara ne bayan sun tashi kunnen doki maras ci da kasar Girka, a wasan Lahadin karshen mako.

Girka dai ta yi kokarin samun jimillar kwallaye 4-1 ne a wasan na karshen kamo, bayan da ta rasa nasara a zagayen farko na wasan da suka buga a makon da ya gabata a Zagreb. Sai dai kuma rashin nasarar hakan ya sanya Croatia samun wannan gurbi na buga gasar cin kofin duniya na shekarar 2018 dake tafe. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China