Yayin wasan karshe da Kenyar ta buga, ta doke tawagar kungiyar Zanzibar da ci 3 da 2 a bugun daga kai sai mai tsaron gida, a filin wasa na Kenyatta dake Machakos, a gabashin kasar.
Wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar, ta rawaito shugaban kasar na jinjinawa kwazo, da da'a, da jajircewa da 'yan wasan kungiyar ta Harambee stars suka nuna, wanda hakan ya kai su ga samun nasara.
Shugaba Kenyatta ya ce "a madadin gwamnatin mu, ina taya kungiyar kwallon kafar kasar mu murnar lashe wasannin ta tun daga zagayen farko har zuwa wasan karshe na gasar CECAFA. Lallai kun sanya mu alfahari da wannan nasara,".
Shugaba Kenyatta ya kara da cewa, nasarar da Harambee Stars ta samu na nuna cewa, jajircewa da cikakken tsari, zai baiwa kasar sa damar kasancewa zakarar yankin da ta ke a fannin wasan kwallon kafa.
Daga nan sai ya jaddada kudurin gwamnatin sa, na ci gaba da tallafawa bunkasar wasanni, a wani mataki na zakulo masu hazaka a fannonin wasannin daban daban, ta yadda hakan zai bada damar tallafar rayuwar matasan kasar.
Harambee Stars ne dai suka fara jefa kwallo a ragar Zanzibar mintuna 7 da take wasa. Sai dai mintuna 3 kafin tashi daga wasan sai dan wasan Zanzibar Khamis Mussa ya farke kwallon.
Cikin minti na 8 na karin lokaci da aka yi ne kuma Masud Juma na Kenya ya karawa Zanzibar kwallo ta biyu a raga, kana mintuna 2 bayan hakan sai dan wasan Zanzibar Khamis ya farke wannan kallo. Wanda hakan ya kai ga bugun daga kai sai mai tsaron gida.
A bugun daga kai sai mai tsaron gidan ne kuma mai tsaron ragar kungiyar Kenya ya ture kwallaye 3, inda aka tashi Kenyan na da kwallaye 3 Zanzibar na da 2.(Saminu Alhassan)