Morocco ce zata karbi bakuncin gasar wasannin na cin kofin Afrikan daga ranar 12 ga watan Janairu zuwa 4 ga watan Fabrairu, wanda ake saran 'yan wasa daga nahiyar ta Afrika zasu nuna bajintarsu.
A wasan da aka buga a katafaren filin wasa na Marrakech Grand Stadium, Momodou Ceesay yayi nasarar zarawa Gambiya kwallaye biyu bayan fara wasan da mintoci 11 da kuma mintoci 38, yayin da Ahmed Hamoudane ya ciwa Morocco kwallo guda mintoci 45 da fara wasan.
A yunkurinta na neman shiga gasar wasannin cin kofin kasashen Afrika na shekarar 2018, kungiyar wasan kwallon kafa ta Morocco ta yi galaba akan takwararta ta Mauritania da ci 4-2 a ranar Juma'a.
Amma ga kasar Gambiya, nasarar data samu a wasan share fagen cin kofin kasashen Afrika na 2018, wanda tayi galaba kan Algeria a wasan da suka buga a watan Maris, ya kasance a matsayin wata dama ce ta shirye shiryen shiga gasar ta kasashen Afrika a shekarar 2019.(Ahmad Fagam)