171026-Ronaldo-ya-lashe-kyautar-kwarzon-dan-kwallon-duniya-na-hukumar-FIFA-zainab.m4a
|
Ronaldo wanda shi ne ya lashe wannan lamba a bara, ya sake samun nasarar hakan a karo na 5, kamar dai yadda abokin takarar sa na kungiyar Barcelona Messi shi ma ke rike da wannan lamba har karo 5.
Hukumar FIFA dai ta matsar da bikin ba da wannan lamba ne zuwa watan Oktoba maimakon Janairu, domin ba da damar zabar dan wasan da ya yi fice a wasannin nahiyar Turai gaba daya, maimakon bin tsarin kalanda na shekara kawai.
Ronaldo mai shekaru 32 da haihuwa, ya jinjinawa wadanda suka zabe shi a bana. Ya kuma yaba wa sauran 'yan takara Leo Messi da Neymar, da duk abokan taka leda da kungiyar sa Real Madrid bisa irin goyon bayan da suka nuna masa.
Ya ce "mun zo Ingila a karon farko, inda na samu wannan nasara a karo na biyu a jere. Na yi farin ciki matuka, wannan lokaci ne na musamman gare ni. Na san ina da magoya baya a dukkanin sassan duniya.
Ronaldo dai ya kasance kan gaba wajen jagorantar Real Madrid zuwa lashe gasar cin kofin zakarun turai ta UEFA, da gasar zakarun kungiyoyin kasar Sifaniya na La Liga. Ya kuma ci kwallaye biyu a wasan karshe na cin kofin zakarun turai, inda Madrid din ta zurawa Juventus kwallaye 4 da 1 a filin wasa na Cardiff.
Sauran wadanda suka samu lambobin yabo a yayin bikin sun hada da koci Zinedine Zidane na Madrid, wanda aka zaba gwarzon mai horas da 'yan wasa. Sai Lieke Martens da aka zaba a matsayin gwarzuwar 'yar kwallon duniya ajin mata, da Sarina Wiegman kocin da ta yi fice a ajin na mata。 Kaza lika a karon farko, an zabi Gianluigi Buffon a matsayin fitaccen mai tsaron gida na duniya. Wannan ne dai karon farko da aka shigar da wannan lamba cikin jerin lambobin yabon da FIFA ke bayarwa.
A daya hannun kuma, FIFAr ta jera Buffon, da Ronaldo, da Sergio Ramos, da Marcelo, da Toni Kroos, da Luka Modric, da Dani Alves, da Leonardo Bonucci, da Andres Iniesta, da Messi da Neymar, a matsayin taurarin 'yan wasan duniya na bana.
Dubun dubatar masu sha'awar kallon kafa ne dai daga sassan duniya daban daban, suka jefa kuri'un su, domin fidda gwanayen da hukumar ta FIFA ta karrama.
Shi ma dan wasa daga kasar Faransa Olivier Giroud, ya tashi da lambar yabo, ta wanda ya ci kwallo mafi kayatarwa a bana, yayin wasan da kungiyar sa ta Arsenal ta doke Crystal Palace a gasar firimiyar kasar Ingila. An kuma karrama magoya bayan kungiyar Celtic a karo na biyu a jere, saboda da'ar su, da nishadantar da masu kallo wasannin kungiyar su.(Saminu Alhassan)