Da sanyin safiyar Larabar nan ne aka kaddamar da harin kunar bakin wake a arewacin kasar Kamaru, lamarin da ya sabbaba rasuwar maharin tare da wasu fararen hula 4.
A cikin watanni 5 da suka gabata, mayakan kungiyar Boko Haram sun kai hari a kalla sau daya a ko wane mako a yankin arewa mai nisa na kasar ta Kamaru, wanda bisa jimilla fararen hula a kalla 158 suka rasu sakamakon hare haren. (Tasallah Yuan)